Home Siyasa Zulum ya bayar da umarni a buɗe ofishin NNPP a Borno

Zulum ya bayar da umarni a buɗe ofishin NNPP a Borno

0
Zulum ya bayar da umarni a buɗe ofishin NNPP a Borno

 

 

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarni bude ofishin jam’iyyar NNPP da ke jihar ba tare da bata lokaci ba.

BBC Hausa ta rawaito cewa a yau Juma’a ne, gwamnan ya umarci hukumar raya birane ta jihar ta bude ofishin.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da fitar a ranar Jumma’a, inda ya ce bayan gwamnan ya samu labarin rufe ofishin ne ya bayar da umarnin bude shi.

Babagan Umara Zulum ya ce ko ma mene ne dalilin daukar matakin bai kamata a rufe ofishin a wannan lokaci ba.

Cikin sanarwar, Malam Isa Gusau, ya ce dama al’ummar jihar na da masaniya a kan cewa tun shekaru uku da suka wuce hukumar raya biranen jihar ke daukar matakan kawo gyara ciki har da rufewa wasu gine-ginen musamman wadanda ba a yi su bisa ka’ida ba.

Hukumar raya biranen ta ce ta daui matakin rufe ofishin ne saboda rashin bin ka’idar da ta dace wajen bude ofishin.

Zulum ya ce sake bude ofishin abu ne da kowa zai so sannan kuma yana da kyau a ba wa kowacce jam’iyya dama gudanar da ayyukanta ba tare da wata matsala ba.

A jiya ne dai hukumar raya biranen da rufe ofishin jam’iyyar wanda ke haɗe da wasu ofisoshinta.

Bayan rufe ofishin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ta NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da rufe hedikwatar jam’iyyar da aka yi.

A cikin wata sanarwa da Kwankwason ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.

An rufe ofishin NNPP ne a yayin da Kwankwason ke shirin zuwa jihar a ƙarshen wannan makon.