Home Labarai Zulum ya fara azumin Ramadan a mahaifarsa, Mafa, inda ya raba N76m da abinci ga mutane 15,327

Zulum ya fara azumin Ramadan a mahaifarsa, Mafa, inda ya raba N76m da abinci ga mutane 15,327

0
Zulum ya fara azumin Ramadan a mahaifarsa, Mafa, inda ya raba N76m da abinci ga mutane 15,327

 

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a yau Asabar ne ya fara azumin watan Ramadan na bana a mahaifarsa, Mafa, a jihar, inda ya shafe daren Juma’a a garin sannan ya tashi da azumi a yau Asabar.

Garin Mafa shine shelkwatar Ƙaramar Hukumar Mafa ce a tsakiyar jihar.

Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Malam Isa Gusau, ya fitar a yau Asabar ta ce gwamnan ya sanya ido a kan rabon kudade, abinci da kayayyakin abinci ga mutane 15,327 da suka hada da ‘yan gudun hijira da kuma sauran talakawa .

Sanarwar ta ce wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da mata 9,313 da maza 6,014; kowanne an ba shi N5,000 jimlar N76,635,000:00.

“Bayan kudin, kowane mutum ya samu shinkafa kilo 50 da yadi biyar na Shadda yayin da kowace mace ta samu nade da sukari kilo 10,” in ji sanarwar.

Yayin da yake garin Mafa, Zulum ya duba kayayyakin aiki a babban asibitin garin, inda ya tattauna da ma’aikatan lafiya.

Gwamnan ya kasance a dakin gwaje-gwaje na asibitin, dakin yin tiyata da kuma wuraren ma’aikata.

Zulum a karshen tantancewar da ya yi, ya umurci babban jami’in kula da lafiya na asibitin da ya gaggauta gabatar da cikakkun bayanai na wasu bukatunsu domin ci gaba da bunƙasa kiwon lafiya a jihar.