
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sauke gaba ɗaya kwamishinonin sa a jiya Alhamis.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwar da Babban Sakataren Gudanarwa da Ayyuka, Danjuma Ali ya fitar a Maiduguri.
Ali ya ce Gwamnan ya amince da sauke ɗaukacin kwamishinonin sa da gaggawa.
Ya yi bayanin cewa gwamnan ya ɗauki matakin sauke kwamishinonin ne domin ya baiwa waɗanda ke da sha’awar tsaya wa takara damar su shiga zaɓukan fidda-gwani masu zuwa a APC.
Ali ya baiyana cewa Zulum ya gode wa kwamishinonin bisa gudunmawar da su ka bayar lokacin da sunkenrike da mukaman, inda ya yi musu fatan alheri a rayuwar su nan gaba.