
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ƙaddamar da wani shiri mai taken “Shirin Taimakon Gwarazan Borno”.
Shirin ya ƙunshi ɗaukar nauyin karatun marayu 500 kyauta da kuma zawarawa da ƴan ƙato-da-gora su ka rasu su ka bari sakamakon yaƙi da ƴan Boko Haram da ISWAP.
Wata sanarwar da kakakin gwamnan, Isa Gusau ya fitar ta ce za a fara shirin ne a watan Janairun 2022.
Ya ce Zulum ya sanar da hakan ne a yayin jawabi bayan danya miƙa kasafin kuɗi na Borno ga Majilisar jihar anjiya Talata.
Ya ƙara da cewa za a kafa kwamiti da zai zaƙulo yara daidai da shekarun firamare da sakandare wadanda ƴaƴan ƴan ƙato-da-gora ne da su ka rasu wajen yaƙi.
Ya kuma baiyana cewa gwamnati za ta kai su makarantun kwaleji na ƙasa da ma makarantun ƙasa da ƙasa su yi karatu a can kyauta.
“Za a yi shirin ne rukuni-rukuni. Yanzu dai za a fara da rukunin yara 500.
” Ƴan bijilant da yawa sun rasa ransu wajen kare jihar nan ta su. Saboda haka dole mu samu hanyar basu ladan aikin da su ka yi.
“Ɗaya bangaren na wannan shiri shine tallafawa zawarawan da a ka mutu a ka bari domin rage musu raɗaɗin tattalin arziƙi,”