Home Cinikayya Wani mahajjaci a ƙasar Saudiyya ya tsinci jakar wata ‘yar Najeriya maƙare da kuaɗe da gwalagwalai

Wani mahajjaci a ƙasar Saudiyya ya tsinci jakar wata ‘yar Najeriya maƙare da kuaɗe da gwalagwalai

0
Wani mahajjaci a ƙasar Saudiyya ya tsinci jakar wata ‘yar Najeriya maƙare da kuaɗe da gwalagwalai

Daga Yasir Ramadan Gwale

Mahajjacin ɗan asalin ƙasar Masar mai suna Lutfi Mohammed Abdelkarim wanda ya je kasar Saudiyya domin aikin hajjin bana na shekarar 1438/2017.

A yayin da mahajjacin ya ke laluben duwatsu domin yin jifan Shedan (jifan jamra), a yayin da yake tsuntar duwatsun da zai yi jifan ne ya hangi wata jaka a gefensa, inda babu kowa a wajen sai shi.

Bayan da mahajjacin ya bude jakar ne yaga gwalgwalai da kudade cike makil a cikin jakar. A yayin da ya zazzage jakar gaba daya ne, yaga wani katin shaida (ID Card) me dauke da sunan wata ‘yar Najeriya.

Mutumin yayi ta cigiyar me wannan jakar a lolacin amma shiru bai sami me jakar ba. Daga nan ne muhajjacin ya nemi jami’an aikin Hajji domin hannanta musu wannan jakar.

Shi dai Lutfi Muhammad Abdelkarim ya samu zuwa hajjin wannan shekarar ne karkashin wani shiri na bakin Khadimul Haramain da ake gayyata daga kasashe daban daban.