
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Saminu Turaki, a ranar Juma’a ya kalubalanci sake mayar da Shari’ar da ake yi masa zuwa babban birnin tarayya Abuja daga katun dake masa Shariah a Dutse.
A lokacin sake zaman kotu zaman kotun mai gabatar da kara, Oluwaleke Atolagbe ya bayyana cewar bban mai sharia’ ya bukace da a mayar da wannan Shariah da ake yiwa Saminu Turaki zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai lauyan da yake kare Ibrahim Saminu Turaki, Olusegun Jolaawo ya kalaubalanci kotun kan batun karar.
Yace daga cikin akwai abubuwan da ya kamata ayi la’akari da shi a wannan Sharia’a. Daga ciki akwai batun, ya kamata kotun ta jira dukkan bangarorin da suke gabanta su yi mata bayani kai tsaye.
Mista Jolaawo ya ga baiken kotun, kan matakin Alkalin kotun Namdi Dimgba kan yadda ya gudanar da Sharia a 18 ga watan Yulin 2017, inda ya bukaci dauke Shariar daga Dutse.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya habaro cewar, Gwamnatin tarayya ce ke kalubalantar Ibrahim Saminu Turaki Shariah kan tuhumce tuhumce guda 32 da ake masa kan zambar kudaden da suka kai Naira biliyan 36.
Ibrahim Saminu Turaki ya aikata wannan almundahana ta wadannan makudan kudade ne a lokacin da yake Gwamnan jihar Jigawa.
NAN