
Kasancewar Nijeriya kasa daya mai cikakkiyar ‘yanci kudira ce ta Ubangiji, a saboda ba kana bane wani ya yi kokarin kawo dalilin rabuwar kasar, inji Shugaba Muhammadu buhari a yau Laraba.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta bakin mataimakinsa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina.
Buhari ya bayyana hakan ne a sakonsa na fatan alheri ga al’ummar addinin Kirista don taya su murnar ‘Ash Wednesday’ (ma’ana ranar kama azumin kwanaki 40 na mabiya addinin Kirista).
Ya yi kira ga ‘yan addinin Kirista da su ci gaba da yi kasar nan addu’ar zaman lafiya da kasancewa kasa daya a koda yaushe.
Ya kuma yi kira ga kafatanin ‘yan Nijeriya da su kaunaci junansu su kuma rike ‘yan uwanta da zumunci tare da kokarin taimakawa masu karamin karfi.
Shugaban ya yi kira ga mabiya addinin Kirista a fadin Nijeriya da su yi koyi da koyarwar Yesu Almasihu, wanda daga wajensa ne azumin na kwanaki 40 ya samo asali.