Home Kanun Labarai Gwamnan Ebonyi ya ja kunnen ’yan PDP su daina zagin Buhari

Gwamnan Ebonyi ya ja kunnen ’yan PDP su daina zagin Buhari

0
Gwamnan Ebonyi ya ja kunnen ’yan PDP su daina zagin Buhari
Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi

Daga Ibrahim Sulaiman

Gwamnan Jihar Ebonyi da ke gabas maso kudancin ƙasar nan, David Umahi, ya ja hankalin ‘yan jam’iyyarsa ta PDP da su daina zagin Shugaba Muhammadu Buhari.

Da yake magana a taron bikin cikar jihar shekara 21 da ƙirƙira a babban birnin jihar na Abakaliki, gwamnan ya shawarci ‘yan PDP da su riƙa yin adawa mai ma’ana.

Umahi, wanda shi ma ɗan jam’iyyar PDP ne, ya ce jam’iyyar adawa kamata ya yi ta riƙa yin hannunka mai sanda ba wai kawai adawa ba gaira ba dalili ba.

“Na sha faɗawa ‘yan jam’iyyata a matakin ƙasa cewa adawar siyasa fa ba da zage-zage ake yin ta ba.

“Haka kuma a matakin jiha zan faɗa muku da ku guji makauniyar adawa,” inji Gwamna Umahi.

Daga nan ne Umahi ya yabi Shugaba Buhari saboda amincewar da ya yi da batun sake yi wa ƙasa garanbawul.

Me za ku ce akan wannan gwamna?