
Sojojin Najeriya sun hallaka wani kwamandan ISWAP, Modu Kime, wanda a ke kira da Abou Maryam a harin jiragen sama da su ka kaiwa ƴan ta’adda a ya kin Tafkin Chadi.
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa gawurtaccen kwamandan na ISWAP ya gamu da ajalinsa ne a luguden wuta da da dakarun Nijeriya su ka yi gaɓar kogin Bisko da Tumbum Tawaye a Ƙaramar Hukumar Abadam.
An kai harin ne bayan da a ka yi shawagi a ka gano inda kwamandan ƴan ta’addan ya ɓoye ya ke kuma shirin kai hare-hare.
An gano cewa an kashe Abou Maryam da sauran mayaƙan sa ne da dama bayan da a ke bibiyar guraren da a ka harba roka-roka ta ƙasa.
Wani jami’i na ɓangaren sintirin sirri ya sahidawa PRNigeria cewa Abou Maryam, mai lambar waya +22788036182, ya daɗe a na fakon shi kafin a kai harin.
“A wasu lokuta mun ɗauki kiran sa na waya in da ya ke haɗa yadda za a kai hare-hare yawanci a Jihar Borno,” in ji majiyar.