Home Siyasa Sheikh Ibrahim Khalil ya bar APC

Sheikh Ibrahim Khalil ya bar APC

0
Sheikh Ibrahim Khalil ya bar APC

 

Fitaccen malamin addinin Muslunci na Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya bar jam’iya mai mulki ta APC a jihar.

Sheikh Khalil, Shugaban Majalisar Malamai ta Arewa, ya sanar da ficewa da ga jami’yar ne a hirar da ya yi da BBC Hausa.

“A matsayi na na ɗan jam’iyar APC kuma ɗaya daga cikin manya a jam’iyar, ina mai sanar da cewa na fita da ga jami’yar.

Sheikh Khalil ya ƙara da cewa “komai ya na da dalili. Akwai dalilai uku amma. Ko masu ilimi su fahimta ko kuma kowa ma ya fahimta.”

Ya ƙara da cewa ficewar ta sa da ga jami’yar bashi da alaƙa da ƙoƙarin cire shi da a ka yi a matsayin shugaban majalisar malamai.

“Ba shi bane dalilin. Tun tuni ma ya kamata a ce na fita da ga jami’yar. Ba sai na ɓata lokaci na ina faɗin dalilin da ya sa na fita da ga gwamnati ba ma,” in ji shi.