
Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids Academy, wanda ya yi garkuwa da ɗalibarsa ƴar shekaru 5, Hanifa Abubakar, ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta 12 da ke Gidan Murtala a Jihar Kano.
Majistare Muhammad Jibril ne ya jagoranci kotun.
An gurfanar da wanda ake zargin ne tare da mutum biyu waɗanda a ke zargin da hannun su a aikata laifin, Hamisu Isyaku da Fatima Jibrin a yau Litinin.
Ƙarar dai ta kasance ne tsakanin gwamnatin jihar Kano da wadanda ake zargin su uku.
A lokacin da aka bukaci a ambaci shari’ar, Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Musa Lawan, Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, wanda ya jagoranci wasu lauyoyi goma sha ɗaya, ya roƙi kotun da ta karanta wa waɗanda a ke tuhumar cikin harshen Hausa domin su fahimta.
Nan take kuwa alƙalin ya amince da hakan.
Bayan karanta tuhume-tuhumen a gaban wadanda ake zargin, ba a ba su umarnin amsa laifinsu ba ko kuma kada su amsa laifinsu saboda kotu ba ta da hurumin yin shari’ar.
Lawan ya kuma roƙi kotun da ta tasa keyar wadanda ake zargin a gidan yari domin baiwa jihar damar shirya tuhume-tuhumen da ake yi musu tare da gurfanar da su a gaban kotun da ta dace domin yanke musu hukunci.
Daga nan ne Alkalin Kotun Mai shari’a Jibril ya bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali na Kurmawa kamar yadda lauyoyin jihar suka bukata sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala shari’ar, Mista Lawan ya bayyana cewa, an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, duk da cewa ba ta da hurumi, saboda ‘yan sanda sun kammala bincikensu, kuma ba su da hurumin ci gaba da tsare su a hannun su.
Ya ƙara da cewa “shi yasa a ka kawo waɗanda a ke zargin kotu domin a samu damar ajiye su a gidan yari kafin lauyoyin gwamnati su shirya takardun tuhume-tuhumen sai kuma a kai su kotun da ta ke da hurumin yin shari’ar.
Ya kuma ci alwashin yin shari’ar cikin kankanin lokaci domin a tabbatar masu laifin sun girbi abinda su ka shuka.