Home Labarai Ƴan bindiga sun kashe mutum 4 tare da ƙona wani gini a Ebonyi

Ƴan bindiga sun kashe mutum 4 tare da ƙona wani gini a Ebonyi

0
Ƴan bindiga sun kashe mutum 4 tare da ƙona wani gini a Ebonyi

 

Al’ummar Ekpaomaka da ke Ƙaramar Hukumar Ikwo ta Ebonyi a yau Laraba sun tashi da tashin hankali yayin da wasu ƴan bindiga su ka dira garin tare da kashe mutane hudu da kuma ƙona wani gini.

Steve Orogwu, shugaban Ƙaramar Hukumar Ikwo ya shaidawa manema labarai cewa ƴan bindigar sun kai hari kan Ekpaomaka, mahaifar sa, inda suka kashe yayansa da ƴaƴansa maza guda biyu da kuma wani mai gadi.

Ya ce maharan sun kuma kona gidan danginsa a harin.

“Sun kai hari gidana da daddare suka kashe babban yaya na da ’ya’yansa maza biyu; sun kashe jami’in tsaron mu tare da kona gidan mu,” inji shi.

Ya ce an ajiye gawarwakin a mutuware a Abakaliki.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a Ebonyi, DSP Loveth Odah, ta ki cewa komai, domin ta ce ba ta yi aiki a hukumance ba.