
Nasiru Koguna ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar ADP a jihar Kano a zaben 2023.
Koguna ya lashe tikitin takarar gwamnan ne ta hanyar maslaha a jiya Litinin a Kano.
Tijjani Lawan, wanda ya sa jagoranci gudanar da zaɓen daga shelkwatar jam’iyyar ta kasa, ya bayyana Koguna a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar.
Ya kuma bayyana Nafiu Haruna a matsayin dan takarar Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Habibu Lawan, Kano ta Arewa da Aliyu Habibu, Kano ta Kudu.
Lawan ya kara da cewa jam’iyyar ta cike dukka gurben ƴan takarar 24 na majalisar wakilai da na majalisar jiha 40.
A jawabinsa, Koguna ya nemi gudunmawar ‘ya’yan jam’iyyar domin samun nasarar ta a zaɓen 2023.