
‘Yan sanda a Anambra sun ceto wasu ƴan mata 35, da ga shekara 14 zuwa 17 da ake zargin ana amfani da su a matsayin bayi na yin jima’i.
DSP Toochukwu Ikenga, mai magana da yawun ‘yan sanda a Anambra ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Awka a jiya Laraba.
Ikenga ya ce huɗu daga cikin waɗanda aka ceto na dauke da juna-biyu.
Ya bayyana cewa an kuɓutar da su ne daga wani otal da ke Nkpor a Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa a jihar.
Ya ƙara da cewa ƴan sanda sun yi wa otal ɗin ƙawanya a ranar 13 ga watan Yuni, inda su ka kuɓutar da ƴan matan da ake amfani da su a matsayin bayi na jima’i, karuwai da masu haifar jarirai domin kasuwancin su.
“Jami’an sun ceto ‘yan mata 35 kuma hudu daga cikinsu na da juna-biyu; wadanda abin ya shafa za a mika su ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa domin a duba su a kuma inganta rayuwarsu,” inji shi.
Ikenga ya kuma bayyana cewa an kama mutane uku da a ke zargin su na da alaƙa da aikata laifin kuma an ƙwato bindigogi guda uku, harsashi bakwai da kuma kuɗaɗe.
“’ƴan sanda sun kama mutum uku sannan sun kwato N877,500,” inji shi.
Ikenga ya ƙara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike.