
Daga Mustapha Buhari, a Maiduguri
Sojojin Najeriya sun harbe ‘yan ƙungiyar ta’addacin nan ta Boko Haram guda biyu a ƙauyen Mayanti dake Ƙaramar Hukumar Bama a Jihar Borno.
Kakakin Runduna ta Bakwai ta Sojin Najeria Laftal Kanal Kingsley Samuel ya shaidawa manema labarai a garin Maiduguri cewa sojojin sun yiwa ‘yan ta’addan kwanton ɓauna a yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa dajin Sambisa.
A cewarsa, an bawa yan Boko Haram ɗin kashi ne a ranar Juma’a 6 ga watan da muke ciki da misalin 10: 45 na dare.
Ya ce bayan biyun da suka bindige, an yi wa ragowar da su ka tsere jina-jina.
Laftanal Kanal Kingsley ya ƙara da cewa sun ƙwato kayan abinci daga wajen ‘yan ta’addar.