
Shirin Dabarun rage Talauci da Bunƙasar Arziki na Kasa, NPRGS, ya ce an amince da Naira biliyan 400 don shirin rage radadin talauci daban-daban a shekarar 2022.
Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya bayyana haka yayin zanta wa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan taron kwamitin gudanarwa na NPRGS na kasa a jiya Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A shekarar 2021 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da NPRGS, wanda mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo zai jagoranta.
Sule ya ce taron an yi shi ne domin duba yadda za a aiwatar da abin da aka amince da shi a cikin kasafin kudin.
“Taro ne na kwamitin gudanarwa na dabarun yaƙi da talauci da bunƙasar arziki na shugaban kasa.
“Taro na karshe da muka yi, taro na hudu, mun samu damar kafa kungiyoyin aiki daban-daban wadanda za mu shirya jimillar kasafin kudin da ake bukata.