Home Labarai INEC ta fara bincike kan katikan zaɓe da ake zargin an binne su a rami

INEC ta fara bincike kan katikan zaɓe da ake zargin an binne su a rami

0
INEC ta fara bincike kan katikan zaɓe da ake zargin an binne su a rami

 

 

 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta fara gudanar da bincike cikin gaggawa kan faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo na katikan zaɓe na dindindin, PVC, da ake zargin an binne a karkashin kasa a wasu wurare, ciki har da harabar gidan wani babban mutum a ƙasar nan.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Festus Okoye, Kwamishinan INEC na Ƙasa, kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa kuri’a, ya fitar a Abuja a jiya Alhamis.

Okoye, wanda ya ce an ja hankalin hukumar ne kan faifan bidiyon, ya tabbatar da cewa INEC ba ta ɗaukar irin waɗannan zarge-zargen da wasa.

“Mun fara gudanar da bincike cikin gaggawa kuma duk wanda aka samu da laifi a cikin wannan makircin da ƙarara ya nuna aniyarsa ta tauye wa ƴan Nijeriya hakkin su na zaɓe, to za a hukunta shi a karkashin doka.

“Duk ɗan Nijeriya da ya cancanta da ya yi rajista a matsayin mai jefa kuri’a, yana da hakkin ya mallaki PVC. Ƴancin da tsarin mulki ya ba shi na kaɗa ƙuri’a a kowane zaɓe bai kamata a yi yunƙurin tauyewa ko tauye shi ta kowace hanya ba.

“A game da bayanan hukumar, an buga katin zabe na PVC ga duk masu rajista a Najeriya har zuwa ranar 14 ga Janairu, 2022, kuma an kai su ga dukkan jihohin tarayya domin karɓa.

OKoye ya yi gargadin “Ba za mu bari wasu ɓatagari su yi wa kokarinmu zagon kasa ba,” in ji Shi.