
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka zana Jarrabawar Kammala Sakandare ta Yammacin Afirka ta 2022 (WASSCE).
Da yake jawabi ga manema labarai a yau Litinin, shugaban ofishin WAEC na kasa, Patrick Areghan, ya ce an fitar da sakamakon ne kwanaki 45 bayan kammala jarrabawar karshe.
An kwashe makonni shida ana gudanar ta tsawon makonni shida daga 16 ga Mayu zuwa 23 ga Yuni, 2022.