
Hukumar kula da gidajen adana kayan tarihi ta Najeriya ta yi maraba da shirin BIrtaniya na mayar wa kasar wasar muhimman kayayyaki da aka sace a karni na 19 daga wurin da ada ake kira Daular Mulkin Benin.
Wani lauya mai ba hukumar ta Najeriya shawara, Babatunde Adebiyi, ya gaya wa BBC cewa yana sa ran za a gabatar da wasu daga cikin kayayyakin 72 nan gaba a Najeriya.
A jiya Lahadi gidan adana kayan tarihi na Horniman da ke London ya ce yana ganin abu ne da ya dace a mayar da kayan.
Kayayyakin sun hada da zanen hotuna na tagulla na Benin da kuma mukullin fadar sarki Uwangue na Daular.
Mista Adebiyi ya ce hukumar ta Najeriya ta kuma cimma yarjejeniya da wasu dakunan adana kayan tarihi na Amurka da hukumar birnin Glasgow domin mayar wa da kasar wasu kayayyakin da aka sace suma a wannan shekara.