
Rundunar ‘yan-sandan Najeriya a Jihar katsina ta ce jami’an tsaro sun hallaka ‘yan ta’adda da ba a tantance yawansu ba a yayin musayar wuta biyu a yankin Karamar Hukumar Kurfi a yau Litinin.
An yi ba-ta-kashin ne a kauyukan Dadawa da Barkiya na karamar hukumar, kamar yadda kakakin rundunar Gambo Isah ya bayyana, a rahoton da jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 1.30 na rana, kuma an yi nasarar kwato tumakai 74 da awakai 34 da kuma shanu biyu da ‘yan ta’adar suka sata.
Kakakin ya ce rundunarsu ta samu kira ne na taimakon gaggawa cewa wasu ‘yan ta’adda da suka kai 80 a kan babura dauke da makamai sun kai hari kauyukna na Dadawa da Barkiya.
Ya ce da samun kiran ne suka tura jami’ansu na musamman wadanda suka shiga musayar wuta da su, inda suka kashe wasu tare da raunata wasu.
Har zuwa lokacin da yake bayar da labarain ya ce jami’ansu na can suna bincike dajin domin kama wadanda aka runata cikin ‘yan ta’addar.
BBC Hausa