
Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani a kan ikirarin da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya yi cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya hana a dauki mataki kan Fulani makiyaya da ake zargi da tayar da hankali a jiharsa.
Gwamnan ya fada wa kafafen watsa labarai cewa wani babban jami’in tsaro ya sanar da shi cewa Shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar kada su dauki matakin murkushe Fulani makiyaya da ake zargin suna da hannu a tashin hankalin baya baya nan.
Fadar shugaban kasa ta ce ba ta ji dadin kalaman da suka fito daga bakin gwamnan ba .
Kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin maganar da ba ta da tushe ballantana makama.
Ya kuma kalubanci Gwamna Ortom da ya bayyana sunayen jami’an tsaron da suka fada masa haka.
“Idan yana son ya nuna cewa shi jarumi ne kamar yadda ya yi ikirari to ya bayyana sunan jami’in sojan da ya ba shi wannan labari ko ya yi shiru da bakinsa,” a cewarsa.
Fadar Shugaban kasa ta ce a halin yanzu kasar tana fama da matsalar tashe-tashen hankula, don haka bai kamata ‘yan siyasa su yi amfani da wannan dama ba wajen kawo baraka tsakanin al’umomin kasar.