
Ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a Katsina a zaben 2023, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya ce goyon bayan jam’iyyarsa ta lashe zaɓe ya wuce siyasa, yana mai cewa “Jihadi ne” ma.
Lado ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina, lokacin da ya karɓi bakuncin wasu jam’iyyun siyasa da suka koma PDP a Ƙaramar Hukumar Safana ta jihar.
Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwarsa na cewa da tarin masu sauya sheka a jihar, zai lashe zaben da gagarumin rinjaye.
“A nan Katsina, ba mu da rarrabuwar kawuna a PDP. Na yi takara da wasu mutane uku, amma duk muna tare yanzu. Ɗaya daga cikinsu shi ne mataimaki na takarara a yanzu, dayan kuma yana neman kujerar majalisar tarayya.
Na ƙarshen kuma, a kodayaushe yana tare da mu, kuma duk abin da muke yi, muna tuntuɓar shi kuma yana ba da shawarwari masu ma’ana,” inji shi.
Daily Trust