
Mutane da dama ne ake kyautata zaton sun mutu bayan da wata tankar mai ta fashe a jiya Laraba a garin Ankpa da ke jihar Kogi.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta ce akalla mutane takwas ne aka tabbatar sun mutu, inda ta kara da cewa adadin wadanda suka mutu na iya ƙaruwa.
Stephen Dawulung, kwamandan hukumar FRSC na Kogi, ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da wata tankar mai ta murkushe wasu motoci huɗu ciki har da wata motar bas.
Kamar yadda NAN ta ruwaito, shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya afku ne a lokacin da motar dakon mai ta fadi sakamakon yanayin shanyewar birki.
“Jami’an mu da suka garzaya wajen da lamarin ya faru, sun samu nasarar ceto wasu mutane biyu da suka samu raunuka, sannan aka garzaya da su babban asibitin Ankpa domin samun kulawar gaggawa,” in ji kwamandan rundunar FRSC.
“Sun samu nasarar kwaso gawarwakin mutane takwas da suka kone daga cikin motocin da suka kone da kuma babura da hadarin ya rutsa da su.
“Kamar yadda yake a yanzu, ba mu da tabbacin adadin mutanen da ke cikin motocin da kuma babura da suka yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa.
“Har yanzu muna kokarin sanin hakikanin adadin domin har yanzu wutar na ci gaba da ruruwa.
“Bayan tankar, akwai wata motar bas ta Sharon, motoci uku da babura uku, waɗanda ba za mu iya sanin adadin mutanen da ke cikin su ba kafin aukuwar lamarin.
“Ana gudanar da bincike tare da hadin gwiwar jami’an kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW), domin gano adadin mutanen da ke cikin motar bas ta Sharon kafin faruwar lamarin.