Home Labarai Maulidi: Gwamnatin Zamfara ta raba wa makarantun Kur’ani shanu 97 da buhunan shinkafa 199

Maulidi: Gwamnatin Zamfara ta raba wa makarantun Kur’ani shanu 97 da buhunan shinkafa 199

0
Maulidi: Gwamnatin Zamfara ta raba wa makarantun Kur’ani shanu 97 da buhunan shinkafa 199

 

 

 

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da tallafin buhunan shinkafa 199 da shanu 97 ga makarantun kur’ani a fadin jihar, kamar yadda kwamishinan harkokin addini na jihar, Dakta Tukur Sani Jangebe ya bayyana.

Jangebe, wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar, Sani Nasarawa a wajen kaddamar da rabon, ya bayyana cewa tallafin na nuna goyon baya ne daga gwamna Bello Matawalle ga makarantun kur’ani domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

“Mu na kira ga malamai da su sanya jihar Zamfara musamman, da kasa baki ɗaya a cikin addu’o’insu, musamman a lokutan bukukuwa kamar yadda su ke yi,” inji shi.

Ya taya al’ummar musulmi murnar wannan biki tare da yin kira gare su da su rungumi zaman lafiya da nuna soyayya ga juna ba tare da la’akari da matsayin al’umma, addini ko kabilanci ba.