
Jam’iyyar APC ta rubuta wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC wasika, inda ta bukaci da ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin sahihin dan takarar sanatan Yobe-ta-Arewa a karkashin jam’iyyar, kamar yadda wata babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta bayar.
A ranar 28 ga watan Satumba, wata babbar kotun tarayya, karkashin jagorancin mai shari’a Fadima Aminu ta umarci INEC da ta amince da buga sunan Machina a matsayin wanda ya cancanta kuma zaɓaɓɓen ɗan takarar sanatan Yobe-ta-Arewa a karkashin jam’iyyar APC, inda ta tabbatar da zaben fidda gwani na jam’iyyar da ta gudanar da shi a ranar 28 ga watan Mayu.
Amma sa’o’i bayan abokin hamayyar Machina, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya amince da hukuncin kotun tsakani da Allah, inda shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe, Mohammed Gadaka, ya ce jam’iyyar za ta daukaka kara kan hukuncin.
Sai dai a wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Oktoba, mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu da sakatariyar jam’iyyar, Iyiola Omisore, jam’iyyar ta umurci INEC da ta buga sunan Machina a tasharta kamar yadda kotu ta bayar.