
Farashin hatsi da sauran kayan abinci ya faɗi a jihar Katsina yayin da ake ci gaba da fuskantar taɓarɓarewar kudi a halin yanzu a ƙasar.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya rawaito cewa farashin masara, dawa, gero da wake ya fado idan aka kwatanta da yadda ya kimanin makonni uku da su ka gabata.
Wani mai sayar da hatsi, Haruna Abdullahi, ya shaida wa NAN cewa buhun masara ana sayar da shi kimanin Naira 19,000 a mafi yawan kasuwanni a yanzu, saɓanin tsohon farashin N24,000.
“A yanzu dai ana sayar da buhun masarar a kan Naira 14,000 zuwa kasa, gwargwadon ingancinsa, yayin da tsohon farashin ya kai N18,000.
“Farashin kayan abinci ma ya fi arha a manyan kasuwanni kamar Dandume, Bakori, Danja da sauran wuraren da ake noman hatsi,” in ji shi.
Wani dan kasuwa mai suna Nasir Isa ya shaida wa NAN cewa buhun gero da a da ake sayar da shi kan Naira 24,000 yanzu ya koma Naira 20,000.
Ya kara da cewa buhun wake da a yanzu yana kan farashi tsakanin N28,000 zuwa N30,000, sabanin tsohon farashin tsakanin N34,000 zuwa N36,000, ya danganta da inganci.
Isa ya lura, duk da haka, yawancin manoman hatsi ba sa karɓar kuɗin ciniki ta taransifa daga kwastomomi.
“Kaɗan kaɗan ne manoma masu wayewa ke karɓar kuɗi ta taransifa yayin ciniki.
“Kaɗan waɗanda ke karɓar kuɗin su na sayar da hatsi a farashi mafi yawa. Misali, idan buhun hatsi ya kai Naira 20,000 a matsayin tsabar kudi, zai kai kamar Naira 23,000 zuwa sama, idan za a biya ta taransifa” inji shi.
Duk da raguwar farashin, masu siyar da hatsi sun koka game da ƙarancin tallafi yayin da abokan cinikin ke fuskantar ƙalubale wajen samun kuɗi daga bankuna da kuma masu sana’ar PoS.