
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce saura ƙiris ya bayar da sammacin kama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Godwin Emefiele, biyo bayan wahalhalun da ƴan Nijeriya ke fuskanta na sake fasalin kudin kasar.
Gbajabiamila wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Lanre Lasisi, ya ce majalisar za ta koma zama kafin zaɓen da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, idan CBN ta gaza magance wahalhalun da ƴan ƙasa ke fuskanta.
Ya ce majalisar za ta ci gaba da sanya ido sosai kan yadda CBN ke aiwatar da manufar biyo bayan ganawar da majalisar ta yi da gwamnan na CBN, Godwin Emefiele, kan batun.
Gbajabiamila ya ce ya na gab da rattaba hannu kan sammacin kama Emefiele, biyo bayan gazawarsa da farko a gaban wani kwamitin wucin-gadi na majalisar, sai kuma gwamnan bankin ya bayyana a gaban kwamitin.
“Majalisar wakilai ta shiga tsakani a lokuta da dama. Mun yi ta kiran gwamnan babban bankin na CBN karo na farko, amma ya ki amsa kira , saboda mu na da tambayoyi masu girma gare shi.
“Sai da na bayar da barazanar kama shi kafin ya zo, kuma da bai zo ba da na sanya hannu kan wannan sammacin,” in ji shi.
Ya ce da tuni a tarihin majalisar dokokin kasar, a karo na farko da za a kama wani gwamnan CBN.