
Babbar gadar Jebba zuwa Mokwa hanyar da ta hada jihohin Neja da Kwara ta karya sakamakon wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwana ana yi a ranar Asabar din da ta gabata.
Wannan hanya ce mai matukar muhimmanci tsakann ‘yan kasuwa da suke safara daga kudu zuwa Arewa ko daga Arewa zuwa kudu. Motoci da dama ne suka rasa tudun dafa, inda suka yi cirko cirko suna jifar dauki sakamakon karyewar wannan gada.
A halinyanzu dai motocin da suka dauko kaya daga kudu zuwa Arewa sai sun yi doguwar tafiya kafin su ratsewa hanyar. Kwamandan rundunar kula da hanyoyi ta kasa Bisi kazeem shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadin nan.
A saboda haka ne, ya bayyana cewar akwai bukatar tura karin jami’an hukumar a sabuwar hanyar da direbobi suke ratsewa domin samun saukin wucewar ababen hawa ba tare da samun wata gagarumar matsala ba.