
Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya bayar da sanarwar sallamar kwamaishinoninsa guda 15 a ranar Laraba, bayan da ya kammala zaman majalisar zartarwar jihar tare da kwamishinonin.
Hakan yana nuna, a cikin kwamishinonin jihar 18 da ake da su, yanzu saura guda 3 kacal suka rage a majalisar zartarwar jihar.
Gwamnan ya kuma umarci manyan sakatarorin ma’aikatun da aka sallami kwamishinoninsu da su rike aikin ma’aikatun kafin nada sabin kwamishinoni.
Bayan haka kuma, kakakin gwamnan Jibrin Ndace, ya kara da cewar, an dakatar da zaman majalisar zartarwar jihar har sai an nada sabbin kwamishinoni.
Sannan kuma, gwamnan, ta bakin kakakin nasa, ya yabawa kwamishinonin bisa lokacinsu da suka bayar domin hidimtawa jihar, da kuma gudunmawa da suka baiwa gwamna Abubakar Sani Bello da dukkan goyon bayan da suka bashi.
Har ya zuwa yanzu dai, ba’a bayyana dalilin da ya sanya gwamnan sallamar kwamishinonin a wannan lokacin ba, duba da cewar zaben 2019 na kara karatowa.
Shin ko kuna ganin ya dace ace gwamna ya sallami kwamishinoninsa a wannan lokacin?