Home Labarai Ta’amali da miyagun kwayoyi a unguwanninmu

Ta’amali da miyagun kwayoyi a unguwanninmu

0
Ta’amali da miyagun kwayoyi a unguwanninmu
Cough syrup

Daga Aisar Fagge

Ko shakka babu, labarin da Jaridar Daily Trust ta rawaito na ranar 11-10-2017 na cewa samari da ‘yan mata na jihohin Kano da Jigawa su na kwankwad’ar codein miliyan uku a kowace rana zai tayar da baqanta ran duk wani mazaunin wa’dannan garuruwan. Abinda rahoton yake nuni da shi shine cewa nan da y’an wasu shekaru, wa’dannan garuruwan za su zama sun fi ko’ina yawan mahaukata, jahilai, y’an iska, y’an daba, kuma garuruwan ba za su zaunu ba! Wal’iyazu billah!

Amma ni ina da ja akan alqaluman da suka ba da wannan qididdigar domin rahoton bai fad’i wata sahihiyar hanya da aka bi aka samo wannan adadin ba. Dalilina anan shine, sanin kowa ne yawancin shaye-shaye an fi yin shi a cikin birni. Su kuma mutanen cikin birnin Kano ba su fi mutum miliyan hud’u ba. To acikin miliyan ukun da suka fitar ka bawa Jigawa miliyan d’aya. To ta yaya za ace miliyan biyu daga cikin birnin Kano suke. Ko kuma ka qaddara su ma y’an qauyen yaje musu. To ka basu miliyan d’aya na mashayan, ta yaya za ace miliyan d’aya daga cikin miliyan hudu duk y’an codein ne? Ko akan samu mutum d’aya da shan kwalaba uku ne? Kuma ina batun qanan yara masu mura?

Ba wai ina kore ta’azzarar da shaye-shaye yayi a unguwanninmu ba ne, musamman unguwata Fagge. Wannan unguwa d’aya ce daga cikin unguwannin da ake siyar da wa’dannan mugayen qwayoyi da shaye-shaye. Kuma galiban yaran ba ‘yan unguwar bane. Zuwa suke da ga unguwanninsu da aka hana su siyarwa a can. Kowa ya san wannan: y’an unguwa da hukuma. Amma babu wani ho66asa na azo a gani daga hukumomin yaqi da fataucin wa’dannan abaibad’an don daqile wannan sana’ar.

Abin takaici, tun daga wayewar gari har qarfe d’aya na dare za ka ga yaran nan da jakunkunan ledarsu suna siyar da kayayyakin nan. Motocin gida da baburan Adaidaita Sahu d’auke da y’an mata kyawawa za ka ga suna ta zirga-zirga a unguwar Fagge. Kai daga ganinsu ka ga y’ay’an mala’u. Za ka d’auka d’inki suka kawo ko suka zo kar6a. A’a. Ko d’aya. Qwaya da codein suka zo siya.

Kuma da yake yaran bugaggu ne, da zarar sun ga mutum yayi parking kawai sai kaga sun zo yi me talla. Akwai wani bawan Allah da ya auri wata yarinya a layinmu. Ya zo da mota yayi parking. Ya na bu’de qofa sai d’aya daga cikin yaran nan yazo yace masa, “alhaji qwaya ko codein”? Sai mijin qanwar tamu ya ce masa “ni iyalina na zo d’auka! Sai yaron yace “sorry sorry”. Innalillahi wa innailaihirraji’un!

Laifin waye? Ina mafuta!

Mu ha’du a gaba.