Home Kanun Labarai Saudiyya ce ke horas da ‘yan ta’adda – Babban Limamin Abuja

Saudiyya ce ke horas da ‘yan ta’adda – Babban Limamin Abuja

0
Saudiyya ce ke horas da ‘yan ta’adda – Babban Limamin Abuja
Farfesa Maqari

A zantawarsa da sashen Hausa na gidan rediyon BBC, Babban Limamin Masallacin ƙasa dake Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya zargi ƙasar Saudiyya da taimakawa wajen horas da ‘yan ta’adda.

Maqarin yana bayani ne akan batun cibiyar nan ta Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da Gwamnatin ƙasar Saudiyya ɗin ta ƙuduri aniyar samarwa a birnin Madina mai tsarki.

Sai dai wannan batu ya tayar da kura, musamman masu ganin cewar Maqari bai yi karatu a Saudiyya ba kuma bai taba zaman Saudiyya ba, don haka suke ganin rashin adalci ne yayi magana kan abinda bai da masaniya ta sosai akansa.

Yaya kuke kallon wannan batu?