Home Labarai A shirye nake na tafka muhawara da Buhari – Atiku Abubakar

A shirye nake na tafka muhawara da Buhari – Atiku Abubakar

0
A shirye nake na tafka muhawara da Buhari – Atiku Abubakar

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewar a shirye yake da ya tafka muhawara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shirye shirye zaben Shugaban kasa na 2019.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da Baban kwamitin yakin neman zabensa a matsayin dan takarar Shigaban kasa.

A wajen taron, Atiku ya kalubalanci Shugaba Buhari da ya fito suyi muhawara a gabanin zaben Shugaban masa da za ai a nan da shekarar 2019.