Home Labarai Abuja: An yanke wa matashi hukuncin wata 15 a gidan yari bisa satar Alƙur’ani da waya a masallaci

Abuja: An yanke wa matashi hukuncin wata 15 a gidan yari bisa satar Alƙur’ani da waya a masallaci

0
Abuja: An yanke wa matashi hukuncin wata 15 a gidan yari bisa satar Alƙur’ani da waya a masallaci

Wata kotu da ke zamanta a Lugbe, Abuja, a jiya Talata, ta yanke hukuncin daurin watanni 15 ga wani matashi, Terkaa Akishi mai shekaru 36 da laifin satar Al-Qur’ani biyu da wayar salula a wani Masallaci a unguwar Asokoro a Abuja.

Alkalin kotun, Malam Aliyu Kagarko, ya yankewa Akishi hukunci, bayan ya amsa laifinsa.

Sai dai Kagarko ya ba shi zabin tarar N40,000.

An tuhumi Akishi da laifin shiga waje ta haramtacciyar hanya da kuma sata.

Mai gabatar da kara, Emeka Ezeganya, ya shaida wa kotun cewa Isah Balikisu na Guards Brigade, Asokoro, Abuja, ne ya kai karar a ofishin ƴansanda na Asokoro a ranar 14 ga watan Maris.

Ya ce mai laifin ya kutsa kai cikin wani masallaci da ke wurin, inda ya sace wayar salula da Al-Qur’ani guda biyu.

Mai gabatar da kara ya ce har yanzu ba a tantance darajar kudin kayayyakin da ya sace din ba.

Ya ce an kwato kayan ne daga hannun Akishi yayin da ƴansanda ke gudanar da bincike.

Mai gabatar da kara ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 348 da 287 na kundin laifuffuka.