Home Labarai An yi Allah wadai da yunƙurin rufe wuraren sayar da barasa a Abuja

An yi Allah wadai da yunƙurin rufe wuraren sayar da barasa a Abuja

0
An yi Allah wadai da yunƙurin rufe wuraren sayar da barasa a Abuja

 

Gabanin wani shiri da aka yi na dakatar da da sayar da barasa a wuraren shakatawa a Abuja babban birnin Najerya, masu irin wadannan wuraren sun rubuta wa ministan babban birnin wasiƙa, inda suke nuna kin amincewarsu da shirin.

BBC Hausa ta rawaito cewa masu wuraren sun buƙaci ministan Muhammad Bello ya bi doka, suna bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai ƴanci.

A wata wasika da suka rubuta ta hannun lauyansu Ifeanyi Remy Agu, mutanen sun bukaci ministan ya ja hankalin jami’ansa su daina aiwatar da dokar da aka sanya ta rufe wuraren shakatawa da sayar da barasa daga karf bakwai na yamma.

Ita dai ma’aikatar babban birnin Najeriya Abujan ta ce za ta fara rue wuraren ne domin aiwatar da bincike da kuma samun bayanan irin abubuwan da ake aikatawa a irin wadannan wurare

A jihohin Najirya da dama ma dai an dauki irin wannnan mataki, bayan kai hari, da kuma ajiye abubuwan fashwa.