Home Labarai Aminin Shugaba Buhari ya rasu

Aminin Shugaba Buhari ya rasu

0
Aminin Shugaba Buhari ya rasu
Marigayi AVM Mukhtar Mohammed

Daga Yakubu Fagge

Tshohon Ministan Gidaje da Haɓɓaka Maraya na Tarayyar Najeriya, mai ritaya AVM Mukhtar Muhammad ya rasu.

‘Yan uwan marigayin sun ce AVM Muhammad ya rasu ne a daren Lahadin jiya a birnin Landan.

Marigayi Mukhtar Muhammed dai tsohon soja ne da ya kai muƙamin Air Vice Marshal, wanda shi ne dab da ƙololuwar muƙamin aikin sojin sama.

Bayan taka rawar da ya yi wajen tunɓuke gwamnatin Yakubu Gowon da kawo gwamnatin Murtala Mohammed, an naɗa shi mamba a majalisar koli ta sojoji wato Supreme Military Council ta wancan lokacin.

Daga bisani an naɗa marigayin gwamnan soja na Jihar Kaduna a watan Yulin shekarar 1978 zuwa watan Oktobar 1979 a lokacin ya na riƙe da muƙamin Wing Commander.

Marigayin ya taɓa riƙe guda cikin kotunan da su ka yankewa ‘yan siyasar Jamhuriya ta Biyu hukuncin zaman daɓaro a gidan kaso sakamakon rashawa da ake zargin su da ita.

Marigayi AVM Muhammad na daga cikin waɗanda su ka ƙirƙiri ƙungiyar Amintattun Buhari wadda aka fi sani da TBO, ƙungiyar da ta taka rawa a wajen tallata shugaban a can baya.

Kafin rasuwarsa, yana riƙe da sarauta ta Wazirin Dutse sannan kuma shine shugaban hukumar daraktocin gidan rediyo mai zaman kansa na farko a Kano, wato Freedom Radio.

Har ila yau shi ne shugaban kwamitin jagoranci na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin amintattu na Arewa Consultative Forum.

Marigayin dai ya jima yana fama da ciwon sankara wanda a ƙarshen nan sai daya shafe kusan wata guda a can Birtaniya ya na amsar kulawa.

Ana sa ran dai kawo gawar mariganyi AVM Mukhtar Muhammad mairitaya Kano yau zuwa gobe daga can ƙasar Ingilan.