Home Ra'ayi Ƴansanda sun kuɓutar da matar aure da akai garkuwa da ita a Kaduna

Ƴansanda sun kuɓutar da matar aure da akai garkuwa da ita a Kaduna

0
Ƴansanda sun kuɓutar da matar aure da akai garkuwa da ita a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kubutar da wata matar aure da aka yi garkuwa da ita a safiyar yau Lahadi.

Kakakin rundunar ƴansandan, ASP Mansur Hassan ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a yau Lahadi a Kaduna.

Hassan ya ce da misalin karfe daya na safiyar yau Lahadi ne jami’an ƴansanda suka samu rahoton cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki wani gida a unguwar Dogarawa a karamar hukumar Sabon Garin Zariya.

“daga nan ne sai masu garkuwa da mutanen su ka yi garkuwa da wata matar aure mai shekaru 37 a gidan.

“Da samun wannan kiran, sai tawagar mu ta ƴan sintiri su ka garzaya wurin da lamarin ya faru suka bi sawun barayin. Saboda karfin wutar da muka sakar musu, sai su ka jefar da wacce su ka sace, wanda ya kai ga ceto ta.”

Ya ce tuni aka kaita wajen ƴan uwanta cikin koshin kafiya ba tare da wani rauni ba.

Hassan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike, yayin da kuma aka kara kaimi wajen cafke wadanda suka tsere domin fuskantar fushin doka.