Home Labarai Ɓarayin wayar wutar lantarki sun faɗa komar ƴan jami’an tsaro a Kano

Ɓarayin wayar wutar lantarki sun faɗa komar ƴan jami’an tsaro a Kano

0
Ɓarayin wayar wutar lantarki sun faɗa komar ƴan jami’an tsaro a Kano

 

Dakarun sintiri na Hukumar Tsaron Faraen Hula, NSCDC, wacce a aka fi sani da ‘Civil Defence’ sun cafke ɓarayin wayar lantarki a Karamar Hukumar Kura da ke Jihar Kano.

Kwamandan rundunar a Kano, Adamu Idris Zakari ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a yau Talata.

Zakari ya ce an kama Surajo Tanimu da Ghali Ali da ɗauri-ɗauri na wayoyin lantarkin, ƙirar ‘Armo’ mai kimanin tsahon mita 8, wacce darajarta ta kai kimanin naira miliyan 1.

Ya ce, kamen ya biyo bayan bayanan sirri da korafi da suke samu daga mahukuntan Babban Asibitin Kura game da sace-sacen kayan wutar lantarki a yankin.

Bayanai sun ce, sakamakon wannan ce, rundunar ta samu nasarar kama su biyun

“Mun fara bincike, kuma muna masu tabbatarwa da al’umma za mu samo wadannan masu laifi domin gurfanar da su a Kotu, a cewar Kwamanda Zakari.