
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa.
Abubakar ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a sahihan shafukansa na ƙafar sadarwa.
Ya ce: “Na yi farin cikin sanar da Gwamna @IAOkowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban kasa.
“Ina sa ran zamu zagaya ƙasa tare, mu gana da ƴan ƙasa tare da gina makoma daya ta zaman lafiya, hadin kai, da wadata ga kowa. Da haɗin kai za mu iya cimma nasara. #Najeriya daya.”