Home Labarai Badakalar Ganduje: Sheikh Ahmad Gumi yayi kaca kaca da Gwamnan Kano

Badakalar Ganduje: Sheikh Ahmad Gumi yayi kaca kaca da Gwamnan Kano

0
Badakalar Ganduje: Sheikh Ahmad Gumi yayi kaca kaca da Gwamnan Kano

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a jihar Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi kaca kaca da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje kan wasu bidiyoyinsa da aka wallafa yana karbar rashawa daga hannun ‘Yan kwangila.

A lokacin da yake jawabi kan batun a Masallacin tunawa da Sarkin Musulmi Bello, Sheikh Ahmad Guminyace ba daidai bane Ganduje ya cigaba da rike mukamin kujererar Gwamnan Kano alhali yana karkashin wannan badakala.