Home Labarai Bai kamata Obasanjo ya ji tsoron EFCC din da ya kafa ba – Gwamna Fayose

Bai kamata Obasanjo ya ji tsoron EFCC din da ya kafa ba – Gwamna Fayose

0
Bai kamata Obasanjo ya ji tsoron EFCC din da ya kafa ba – Gwamna Fayose

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yayi dirar mikiya akan tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo. Fayose ya bayyana cewar matukar Obasanjo yana jin cewar shi mai gaskiya ne to bai kamata ya tsorata dan ana yi masa barazanar za’a kama shi ba.

Fayose yana yin wannan magana ne bayan da a makon nan tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya bayyana cewar take taken Gwamnatin Shugaba Buhari tana yunkurin kma shi domin bincikarsa.

Tun kwanaki dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi tsohon SHugaban kasa OObasanjo da yin almubazzaranci da dukiyar Najerya wajen biliyan goma sha shida na dalar amurka domin samarda wutar lantarki, wanda yace babu kudin babu kuma wutar lantarkin ya zuwa yanzu.