Home Kasuwanci Bankin Raya Ƙasashen Afirka zai tallafawa Kano da dala miliyan 110

Bankin Raya Ƙasashen Afirka zai tallafawa Kano da dala miliyan 110

0
Bankin Raya Ƙasashen Afirka zai tallafawa Kano da dala miliyan 110

 

Bankin raya ƙasashen Afirka, da ake kira ‘Africa Development Bank’ ya baiyana cewar zai kashe zunzurutun kuɗi sama da dalar Amurka miliyan ɗari biyar a jihohin Najeriya.

Daga cikin adadin kuɗi, bankin ya shirya kashe dala miliyan ɗari da goma a Jihar Kano.

Shugaban bankin, Akinwumi Adesina shi ne ya baiyana haka a Kano yayin da ya ziyarci Glgwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje bayan da ya je yi wa Aliko Ɗangote ta’aziyar rasuwar ɗan’uwansa, Sani Gote.

Adesina ya baiyana cewar za su kashe waɗannan kuɗaɗen ne a fannin noma da gina hanyoyi a birni da karkara da kuma harkar lafiya a dukkan faɗin jihar Kano.

A yayin da ya ke jawabi, Ganduje ya nuna godiya da jin daɗinsa ga wannan tallafi da bankin zai bayar.

Haka kuma, gwamnan ya tabbatarwa da Shugaban bankin cikakken haɗin kai da kuma goyon baya daga ɓangaren Glgwamnatin jihar.