
Rukunin kamfanin BUA, ya bada tallafin Naira Biliyan 2 don agazawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a birnin Maiduguri na jihar Borno.
A ranar 10 ga watan Satumba ne dai, ambaliyar ruwa ta raba dubban mazauna birnin da muhallinsu a yankunan Fori da Galtimari da Gwange da Bulabulin a Maiduguri.
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce sama da mutane 30 ne suka rasu a yayin da sama da mutane dubu 400 suka rasa gidajensu.
A wata sanarwa a ranar Talata, kamfanin BUA ya mika tallafin kudi na Naira Biliyan 1 don kayan abinci na Biliyan 1 don rage radadi ga wadanda ambaliyar ya shafa.
Kamfanin ya ce, kayan da suka hada da Fulawa da Taliya da Sukari da shinkafa za a bayar da su ga yankunan da abin ya shafa don saukaka musu radadi.
Da yake jawabi a yayin ziyarar jaje da kamfanin ya kai Maiduguri, Abdul Samad Rabiu, shugaban kamfanin ya ce ambaliyar ta haifar da matsin rayuwa ga dubban iyalai.
Ya ce, BUA zai yi aiki da hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki don tabbatar da an samar da abubuwan yau da kullum don tallafawa mutanen Maiduguri.