
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Gwamnonin Najeriya da Manyan Alkalan jihohi da su gaggauta sakin mutanan da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba, Buharin yana bayyana hakan ne a yunkurinsa na kawo sauyi a fannin shari’ah.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yau litinin a birnin tarayya Abuja. Yace tun watan da ya gabata na bayar da umarnin a saki mutanan da suke tsare a gidajen kason kasarnan ba tare da shari’ah ba. Ya kara da cewar, cikowar da ake samu a gidajen yari da tsaaikon gudanar da shari’ar wadan da suke tsare na haifar da rashin yadda ga tsarin shariar kasarnan.
Buhari na magana ne a yayin bude taron gamayyar Alkalan manyan kotunan Najeriya na shekarar 2017 da ake gudanarwa a birnin tarayya Abuja.
Taken taron gamayyar na bana dai shi ne “Karfafa tsarin shari’ah da tabbatar da bin gaskiya da kiyaye doka da bin tsari”.Taron na zuwa ne a daidai lokaccin da Demokaradiyyar Najeriya ke kara yin karfin, yayin da shari’u sukai yawa a kotuna.
Ya cigaba da cewar, al’umma na fatan samun adalci a yayin kowacce shariah, da kiyaye gaskiya da baiwa mai hakki hakkinsa, domin hakan shi ne adalci da zai kawo aminci da nutsuwa.
“Abin takaici kotunanmu sai su yi ta jan shari’ar da bata kai ta kawo ba, zuwa tsawon Shekaru babu gaira babu dalili, wanda hakan ke jefa shakku kan irin wadannan shari’o’i da al’umma ke fuskanta a kotuna daban daban.
Akwai tarin shari’o’i da suke nan jibge da ba a kula su ba, musamman a kotunan daukaka kara.
Fatana sauye sauyen gudanar da shari’o’in kasarnan ya samar da tsarin da zai haifar da saurin aiwatar da shri’un da suke gaban kotunan kasar nan, domin mutanan da ba su da galihu su san cewar ana yi musu adalci a shariah..
Buhari ya bukaci Alkalai da su yi dukkan mai yuwuwa wajen sanya gamsuwa da nutsuwa a zukatan al’umma dangane da Shari’un dake gaban kotuna a tsarin da ake na samar da sauyi a shari’un Najeriya.
NAN