Home Kanun Labarai Buhari ya nemi afuwar Saraki da Dogara kan tare musu hanya da akai a fadar Gwamnati

Buhari ya nemi afuwar Saraki da Dogara kan tare musu hanya da akai a fadar Gwamnati

0
Buhari ya nemi afuwar Saraki da Dogara kan tare musu hanya da akai a fadar Gwamnati
Shugaban ƙasa da mataimakinsa, tare da Shugabannin majaalisun dokoki na ƙasa suna tattaunawa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi afuwar Shugabancin Majalisun Dattawa da na tarayya akan soke liyar da ya shirya musu da yayi a karon farko.

Da farko an tsara cewar, Shugaba ƙasa zai marabci shugabannin majalisaun dokoki na ƙasa domin liyafar cin abinci dare a fadar Shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 8:30 na daren Alhamis. Amma daga bisani aka ce an soke wannan liya, kuma jami’an tsaro suka shana shugabannin shiga fadar ta shugaban ƙasa.

Sai dai daga bisani, Shugaban ƙasa yayi ganawar sirri da shugabannin majalisar a gidansa na musamman dake fadar ta shugaban ƙasa, ya gane da Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai ta ƙasa Yakubu Dogara da mataimakin shugaban ƙasa da kuma wasu na kusa da Shugaban.

Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Mista Femi Adesina, ya gayawa manema labarai a fadar ta shugaban ƙasa a daren jiya cewar, Shugaban ya nemi afuwar Bukola Saraki da Yakubu Dogara ne bayan da suka fito daga wata ganawar sirri a gidansa dake fadar gwamnatin.

Ya ƙara da cewar, Shugaban ya sake sanya ranar 31 ga watan Oktobar nan domin yin liyafar da ‘yan majalisun dokokin.

Sai dai, kamfanin dillancin Najeriya NAN yace an soke liyafar ne sakamakon rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin jami’an tsaron fadar Shugaban ƙasa da kuma ‘yan majalisar a babbar hanyar shiga fadar Gwamnatin.

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewar, rashin fahimtar junan ta faru ne, sakamakon buƙatar da jami’an tsaron fadar shugaban ƙasa suka yi na ‘yan majalisar da su sauko daga cikin motar da ta dauko su, domin a tantance su, su kuwa ‘yan majalisar suka ce sai dai su koma akan a tantance su kawai dan sun zo amsa gayyatar da shugaban ƙasa yayi musu.

An tsara cewar, idan ‘yan majalisar sun zo shugaban ƙasa zai yi amfani da wannan damar domin tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi ƙasa, ciki har da batun kasafin kudi na 2018.

Tuni dai aka amince da daftarin kundin kasafain a zaman majalisar zartarwa da Shugaban ƙasa ya jagoranta a fadar gwamnati a ranar Alhamis din.