Home Labarai Cutar ƙyanda ta kashe yara 14 a Anambra

Cutar ƙyanda ta kashe yara 14 a Anambra

0
Cutar ƙyanda ta kashe yara 14 a Anambra

 

Gwamnatin Anambra ta tabbatar da mutuwar yara 14 sakamakon ɓarkewar cutar ƙyanda a ƙananan hukumomi tara na jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Afam Obidike ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai kan yaƙi da cutar kyanda a Awka a yau Laraba.

Ya ce an samu sabbin kamuwa da cutar ƙyanda sama da 414 a kananan hukumomi tara na jihar ba.

Obidike ya lissafa kananan hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Anambra ta Gabas, Anambra ta Yamma, Ayamelum, Ihiala, Idemili North, Nnewi North, Onitsha North, Njikoka, da Oyi.

Kwamishinan ya bayyana cewa tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya taimaka wa jihar wajen daƙile yaɗuwar cutar.