
Dakar Amurka ta tashi zuwa Naira 610 a kasuwar musayar kudin Nijeriya a kasuwar bayan fage, inda bata taɓa yin irin wannan tashin gwauron zabin ba a tarihi.
Duk da cewa farashin naira a hukumance ya daidaita a kan Naira 419.02 a tagar masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, bayan da Dalar ta yi kasa-da-kasa a ranar Juma’a, darajar kudin ta ƙara yin kasa sosai a kasuwar bayan fage.
A cewar Aboki Forex, wani shafin yanar gizo da ke bada bayanan farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje a kasuwannin bayan fage, ana sayar da dala kan N610 a safiyar yau Lahadi.
Aboki Forex ya shahara ne jim kadan bayan da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele ya rufe wani shafin yanar gizo mai kama da shi, mai suna Aboki FX , bisa zargin karkatar da kuɗin musaya a kasuwar hada-hadar kuɗi.
Daga N588 kowacce dala a ranar 8 ga watan Mayu, an bude ta ne akan N610 a safiyar Lahadi, kamar yadda Aboki Forex ya bayyana.