
Kungiyar ma’aikatan man fetur da Gas ta Nijeriya, PENGASSAN, ta bayyana dalilin da ya sa dillalan mai su ka gaza siyan mai kai tsaye daga matatar mai ta Dangote.
Shugaban kungiyar, Festas Osifo a yayin taron manema labarai a Legas a ranar Talata, ya ce batun ya ta allaka ne kan farashin da NNPC ke siyan man fetur da kuma farashin da ya ke siyarwa ga dillalan man.
Osifo ya yi bayanin cewa NNPC ka iya siyan man kan Naira 950 ya kuma ya siyar da shi kan Naira 700 ga dillalan man, wanda ke sanya NNPC ke samun faduwa a cinikin man.
Ya ce, manyan dillalai zasu iya siyan man daga Dangote a farashin da NNPC ke siya amma zasu siyar da shi ne sama da Naira 1, 000.
Ya ce dillalan man sub zabi siya a wurin NNPCL ne don sanun saukin farashi.
Osifo yayi bayanin cewa ana bayar da wani danyen man ne don biyan bashi wanda hakan yake takaita samar da man don amfanin cikin gida.