
Rayuwa na da ban tsoro… in kana cikin daula da natsuwa to ka bi a hankali kayi komi don neman yardar ALLAH, ka mutumta dama ka zauna lafiya da kowa.
Tabbas nishadi da yalwa duk suna iya canza maka a cikin wuni daya, abinda ka saba dashi zai iya sauyawa zuwa wanda baka taba tunani ba. wato daga Bakin ciki ka koma farin ciki, ko daga mai babu ka ko ma mawadaci. Haka nan daga mai mulki kana iya dawowa talaka…
Allah na jarabtar bawa ta ko wanne fanni, don haka a kullum karka ta6a dauka kai kadai ne a yayin da duniya taimaka kunci ko in tayi maka dadi.
Jarabawa ce Allah ya dora maka wani abu da zai zama abin damuwa a gareka dan a ga karfin imaninka a gare Shi. Ka zama mai tawakkali da addu’a, zaka ga sakamakon alheri, amma in kaki natsuwa ka dogaro ga Allah to zaka rayu cikin nadama da masifar rashin godiya ga Allah
Ba lallai bane ace komi ka nema a take zaka samu, ko abinda kake so ya faru a lokaci daya ba, saboda haka kar ka gaza, Ka rike addu’a da sadaka, ka kyautata imaninka, ka yawaita istigfari kuma ka mika lamurranka ga Allah.
Allah ya sa mu dace, Amin