
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce wa’adin ci gaba da yin rajistar katin zaɓe, CVR, yana nan a ranar 31 ga watan Yuli, kuma wadanda suka yi rajista fiye da sau ɗaya to sun lalata rijistar ta su.
Kwamishinan zabe na Birnin, Yahaya Bello, ya bayyana haka a wani taron manema labarai game da shirye-shiryen hukumar na babban zaben 2023, kan aiki rijistar zaɓe, ingancin katin zaɓe da karɓar sa a Abuja.
Bello ya ce za a dakatar da duk wasu ayyukan katin zaɓe in ban da karɓar waɗanda a ka rig aka buga a ranar Lahadi 31 ga watan Yuli, inda ya kara da cewa hukumar ta kara sa’o’in rufewa zuwa karfe 5 na yamma har da ranakun Asabar da Lahadi.
A cewarsa, an yi hakan ne domin a samu taruwar wadanda a yanzu suka gane cewa suna bukatar PVC a sa’ar karshe a aikin da aka kwashe sama da shekara guda ana gudanar wa.