Home Labarai Fashewar tukunyar gas a Kano: Mutane 9 sun mutu 10 kuma sun jikkata –NEMA

Fashewar tukunyar gas a Kano: Mutane 9 sun mutu 10 kuma sun jikkata –NEMA

0
Fashewar tukunyar gas a Kano: Mutane 9 sun mutu 10 kuma sun jikkata –NEMA

 

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane tara, goma kuma sun jikkata sakamakon fashewar tukunyar iskar gas da ta afku a safiyar jiya Talata a titin Aba, Sabon Gari a jihar Kano.

Ko’odinetan hukumar NEMA a jihar Kano, Nuradeen Abdullahi, ya tabbatar wa manema labarai hakan yayin da yake bayar da karin haske kan fashewar tukunyar iskar gas ɗin a Kano a yammacin jiya Talata.

“Mutanen da suka mutu a fashewar iskar gas da ta afku a titin Aba da ke Sabon Gari a karamar hukumar Fagge, Kano, ya karu zuwa tara.

“An samu gawarwaki tara daga wani gini da fashewar ta shafa, kuma an ajiye su a mutuwaren asibitin ƙwararru na rundunar sojoji da ke Kano.

“Mutane goma sun samu raunuka kuma an kai su asibitoci daban-daban, inda biyu daga cikinsu an sallame su,” inji shi.

Ya kara da cewa Darakta-Janar na NEMA, Mustapha Habib ya je wajen da lamarin ya faru.

“Darakta-Janar na NEMA ne ya jagoranci tawagar ceto da kuma masu tono don tabbatar da an kwashe mutanen da suka maƙale a ƙuraguzan ginin.

“Tawagar NEMA ta ceto sun kasance a wurin da lamarin ya faru domin gudanar da bincike tare da gano illar fashewar.”

Abdullahi ya kara da cewa aikin ceton wanda aka fara da misalin karfe 10 na safe kuma aka rufe a hukumance da misalin karfe 5:15 na yamma, an yi shi ne cikin kyakkyawan tsari.